Home Siyasa A Kwai Kuskure A Kasafin Kudin Da Shugaban Kasa Tinubu Ya Gabatarwa...

A Kwai Kuskure A Kasafin Kudin Da Shugaban Kasa Tinubu Ya Gabatarwa Yan Najeriya – Inji Hon. Tukura

144
0
Sen. Tukura 2

Dan Majalisar Taraiya da ke Wakiltar Zuru da Sakaba da ga Jihar Kebbi, Hon. Kabiru Ibrahim Tukura ya ce akwai kuskure a kan Kasafin Kudin da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya gabatar a gaban Majalisar Taraiya ranar Laraba.

Dan Majalisar ya ce ko da ya ke yayi abun a yaba masa na kara kudaden manyan aiyuka amma duk da haka akwai kuskure a fifita kudaden gudanarwa fiye da na gudanar da manya aiyuka. In da ya ce ba wata kasa da za ta samu cigaba idan ta cigaba da gudanar da kasafin kudinta a irin wannan tsari.

Hon. Tukura ya kara da cewa abun a yabawa shugaban Kasar ne idan aka kwatanta yadda Kasafin Kudin da ya gabatar yafi na gwamnatocin da su ka shude kafin zuwan sa yadda ya kara yawan Kudin da za a kashe a wajen manyan aiyuka.

Ya ce koda ya ke Kasafin Kudin bai yi bayanai dalla-dalla ba amma da ga takaitaccen abun da Shugaban Kasar ya gabatar ya dan bayar da haske yadda  Kasafin kudin zai kasance.

Har ila yau, Dan Majalisar ya ce Kasafin Kudin ya zowa Majalisar a cikin kurarren lokaci kuma ya na da wuya a tsefe Kasafin kamar yadda ya kamata idan ana so ayi adalci ga Yan Najeriya sabo da baikamta a yi a gurguje ba amma duk da haka Majalisar zata yi iyacin kokarin ta.

Tukura ya kara da cewa kudaden da aka ce za a samu da ga haraji na cikin gida na sama da naira Tiriliyan 18 shima abun a yaba ne kuma abu ne mai yiwuwa idan aka yi duba da irin kokarin da shugaban Kasar ya yi a lokacin da yana gwamnan Jihar Lagos in da ya rike jihar na shekaru da kudaden da ya ke samu da ga harajin cikin gida.

Bayan haka Dan  Majalisar ya ce ya yi wuri a fara suka ko rashin sukar gwamnatin domin wannan ne karo na farko da shugaban Kasar ya gabatar da Kasafin Kudi sabo da haka idan ana so ayi masa adalci sai a bari ya yi shekara guda sannan sai akwatanta abun da ya yi da wanda ya ce zaiyi.

Ya ce ko da ya ke Yan Najeriya su na cikin wani hali na matsin tattalin arziki amma idan ana so ayi wa Shugaban Kasar adalci akwai bukatar a yi hakuri a ba shi lokaci ya aiwatar da tsare-tsare da ya gabatar kafin a yanke masa hukunci.

Hon. Tukura ya ce sabanin yadda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya rinka yabon shugaban Kasar, Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya gayawa shugaban Kasar gaskiya na halin da Yan Najeriya su ke ciki da bukatar da kawo musu dauki na gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here