Home Siyasa 2023: An Shawarci Matasa Da Ka Da Su Yarda A Tunzura Su...

2023: An Shawarci Matasa Da Ka Da Su Yarda A Tunzura Su Lokacin Zabe

351
0

An yi kira ga matasa da  al’umar Najeriya baki daya da su kaucewa dukkan wani  abu da ka iya tunzura su don ganin an gudanar da zaben da ke tafe cikin kwanciyar hankali da zaman lafia.

Wannan kira ya fito ne da ga Kungiyar da ke Tallafawa Matasa da Rajin Kawo Zaman Lafia wato “Concern Mind for Youth Empowerment and Peace Development Initiative” ta bakin  Shugabanta na kasa, Alh Habibu Sani Kano.

Yace, ya kamata a gujewa duk wani abu daka ‘iya zama bara zana ga Zaman lafiyar wannan kasa tamu. “akwai bukatar  jajircewa da adu’oi adukkan wuraren ibadun mu kama daga Masallatai da Maja’mi’u domin cigaba da dorewar Najeriya a matsayin kasa daya al’uma daya .

Kuma muyi dukkan mai-yuwa wajen baiwa Jami’an tsaro hadin kai adai dai wannan lokaci da muke tunkarar Babban Zaben na kasa”.

Kungiyar ta yi kira ga al’ummar Najeriya da su kasance masu biyayya ga shugabanni musamman al’ummar Arewacin Najeriya duba da yanayin da aka samu kai a ciki na matsin tattalin arziki.

Kano yace, duk da cewa akwai ma bambantan ra’ayoyi dan gane da sauyin fasalin kudin da Babban Bankin Kasa wato (CBN) ya Sanar, akwai bukatar mutane su kara hakuri domin kuwa komai mai wucewa ne kuma bayan tsanani, sauki na nan tafe da yardarm Allah.

Ya kara da  cewa, mahukunta sun sha fadi cewa anyi wannan sauyin kudi ne da kyakkyawar niyya dan dakile ta’addanci da Yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da karbar  kudin fansa da ma  cinhanci da rashawa; hakan ya taba tattalin arzikin talakawa. Sabo da haka sai anyi hakuri sosai.

Ya cigaba da cewa ko shakka babu wajibi ne ajawo hankalin al’uma kan muhimmancin zaman lafia wanda hakan shine ginshikin dorewar demokaradiya.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnati da kuma shugabanni al’umma na bangarori da ban- da ban da su hada hannu wajen gani an samarwa da wannan kasa hanyoyin saukaka mu su irin wahal-halun da ake ciki.

Bayan haka ya roki gwamnati da ta yi dukkan mai-yuwa wajen tabbatar da adalci da kuma kyakkyawan yanayi na kasuwanci musamman dan jawo hankalin masu zuba hannun jari a wannan kasa tamu wanda hakan ka,’iya samar da ayyukan yi a tsakanin matasan Kasarnan baki daya.

Agefe guda kuma, ya yi kira da bankuna da su kasance masu tsari da tabbatar da tsarin kula da Jama’ar da suke hada hadar kasuwanci da su wanda yace, yin hakan zai iya samar da kyakkyawan yanayin mu’amulla da su da abokan ma’amullar ta su.

Daga karshe yace, Najeriya itace uwa ga kasashen Africa, sabo da haka, idan muna so mu cigaba da rike wannan kambu wajibi ne mu kasance kamar wata mahanga ga sauran kasashen Africa ta hanyar nu ni da kyawawan ayyuka da kuma kaucewa dukkan wani abu da ka’iya zama barazana .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here