Home Siyasa ‘Ƙararrakin zaɓe ba za su hana miƙa mulki ga Tinubu ba’

‘Ƙararrakin zaɓe ba za su hana miƙa mulki ga Tinubu ba’

175
0

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ƴan Najeriya cewa duk da kalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da wasu jam’iyyu ke yi ba zai hana ta miƙa wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu mulki ba.

Da yake magana da manema labarai a ranar Talata, shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha, ya ce sun shirya tsaf domin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu cikin tsanaki ba tare da wata matsala ba.

Mustapha ya ce ƙarar da wasu jam’iyyu suka shigar kan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da jam’iyyar APC da kuma INEC ba zai dakatar da shirye-shiryen da suke yi ba.

Ya ce tuni shirye-shiryen kwamitin ya yi nisa, inda ya ce an ɗora wa ƙaramin kwamitin tsaro na miƙa mulkin da ya tabbatar da cewa babu wani mahaluki da zai kawo tarnaki ga shirin miƙa mulkin.

A ranar 9 ga watan Febrairun 2023 ne shugaba Muhammadu Buhari ya amince da naɗin kwamitin wanda aka ɗora wa alhakin gudanar da dukkan ayyukan shirin miƙa mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa.

Mambobin kwamitin sun haɗa da sakataren gwamnatin tarayya wanda shi ne shugaban kwamitin da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Sauran sun haɗa da babban lauyan gwamnatin tarayya da babban sakatare a ma’aikatar shari’a da kuma manyan sakatarori daga waɗannan ma’aikatu na gwamnatin tarayya.

Ƙorafe-ƙorafe

Tuni dai jam’iyyun adawa a Najeriya da ƴan takaransu na shugabancin ƙasa suka garzaya kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na ranar 25 ga watan Fabarairu a kotu.

Jam’iyyun suna ƙalubalantar ingancin zakamakon zaɓen ne bayan da suka zargi INEC da gazawa wajen wallafa sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a rumbun ajiye bayanai kamar yadda ta alƙawurta.

INEC dai ta ce matsalolin da aka samu da na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a ta BVAS ne ya janyo tangarɗar. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here