Home Mulki Ƙaddara ce kawai ke samar da shugabanni irin Buhari – Tinubu

Ƙaddara ce kawai ke samar da shugabanni irin Buhari – Tinubu

212
0
Tinubu Buhari

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a matsayin mai rikon amana, gaskiya da adalci da kuma kishin ƙasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne cikin saƙon murnar ƙarin shekara ga tsohon shugaban ƙasar da ya cika shekara 81 a duniya.

Shugaba Tinubu ya yaba da zarrar ƙwarewar shugabanci da samun nasarori na tsohon shugaban ƙasar, ya kuma tuna da irin ”bautar a zo a gani da ya yi wa ƙasa” a lokuta daban-daban a matsayin shugaban gwamnatin mulkin soja da kuma shugaban ƙasa a ƙarƙashin tsarin dimokuradiyya.

Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa tsohon shugaban ƙasar kan tarin ayyukan raya ƙasar da ya gudanar a ɓangarori da dama zamanin mulkinsa, musamman fannin tsaro da samar da abinci.

Shugaban Najeriyar ya kwatanta tsohon shugaban ƙasar a matsayin kyakkyawan misali na mutum mai halayyar sadaukarwa, da biyayya da nuna ƙauna, da kishin ƙasa, da riƙon amana a tafarkin ci gaban kasa.

”Buhari ya kasance cikin ɗaiɗaikun jajirtattun shugabanni masu amana. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen bauta wa ƙasa, Buhari ya ja wa kansa ɗauri a gidan yari duk don kishi da son bauta wa ƙasa, samun shugabanni irin abokina Buhari, na faruwa ne kawai bisa ƙaddarar ubangiji, mutum ne mai karimci da dattako, idan ya ce zai yi, to zai yi, haka kuma idan ya ce ba zai yi ba, to kuwa ba zai yin ba”, in ji Tinubu. (BBC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here